
‘Yansanda a jihar Ogun a karkashun rundunarsu ta SWAT sun kama wasu mutane da ake zargin suna safarar sassan jikin mutane.
Da farko dai an kama Sunday Akintobi dan kimanin shekaru 36 a Itoku ta garin Abeokuta inda daga baya kuma aka kama karin mutane 2 Oladimeji Olaniran dan shekaru 40 da kuma Isaiah Tijani dan shekaru 38.
Kakakin ‘yansandan jihar, CSP Omolola Odutola, ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an gano wasu abubuwa a gidajen wadannan mutane wanda an yi amannar cewa sassan jikin mutanene.
Yace kwamishinan ‘yansandan jihar ya bayar da umarnin yi bincike kan lamarin.