
Wani matashi dalibin jami’a a kasar Ghana ya kàshè kansa ta hanyar rataya bayan kama budurwarsa na cin amanarsa.
Lamarin ya farune a jami’ar University of Education, Winneba dake kasar ta Ghana ranar Laraba, 16 ga watan Afrilu.
Saidai ba’a bayyana sunan dalibin ba.
Rahotanni sun bayyana cewa, dalibin ya yanke jiki ya fadi bayan kama budurwar tasa inda kuma daga bisani ya shiga daki ya rataye kansa.
‘Yansandan garin Winneba sun dauke gawar matashin inda suka tafi da ita suka fara bincike.