
Wani bayerabe ya fada rijiya a garin Ilorin West na jihar Kwara bayan da ya sha kwaya da ake cewa Colorado.
Ya sha kwayar ne ranar Sallar, watau Juma’ar data gabata inda tasashi ya haukashe ya tuma ya fada Rijiyar.
Sunan mutumin Kareem dan shekaru 43.
Hukumar kwana-kwana ta jihar ta bayyana cewa, an kirata aka sanar da ita lamarin da misalin karfe 10:29 na safe, kamar yanda kakakin hukumar, Hassan Adekunle ya bayyana.
Yace da suka je sun fitar da gawar mutumin inda suka mikata hannun ‘yansanda.