Sunday, December 14
Shadow

Kalli Yanda Zanga-zangar “Takalmin Annabi ya fi kowa” ta barke a Katsina

Daga Auwal Isa Musa

Kamar yadda wakilin Jaridar Taskar Labarai taskar labarai ya aiko mana, cincirindon jama’a ne suka yi farin-dango wajen fitowa tare da bazama a kan manyan Titunan birnin Katsina da hantsin yau Asabar, domin gudanar da zanga-zanga maintaken “Takalmin Annabi ya fi kowa”

Bangarorin al’ummar musulmi a jihar ta katsina, an shaida shigarsu wannan zanga-zanga wadda yanzu haka take gudana a tsanake, a yain da mahalartanta ke rera wakokin yabo ga fiyayyen halitta, musamman Takalminsa (S) da suka fito zanga-zangar nuna daraja da fifikonsa.

Zanga-zangar ta taso ne taso ne daga filin Polo/kofar ‘yandaka, inda ta ta nufo cikin gari.

Karanta Wannan  Wani Kamfanin mai daga kasar waje ya zo kusa dani ya kama hayar matatar man fetur dan ya rika tace man fetur da bashi da inganci>>Dangote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *