Friday, December 5
Shadow

Kamfanonin Rarraba wutar Lantarki ne ke bamu matsala wajan magance matsalar rashin wuta>>Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta koka da cewa, Kamfanonin raba wutar Lantarki, Discos ne ke kawo mata cikas wajan samar da ingantacciyar wutar lantrki a Najeriya.

Ministan Wutar Lantarkin Adebayo Adelabu ne ya bayyana haka yayin ganawa da kwamitin majalisar Dattijai dake kula da makamashi.

Yace kamfanonin rarraba wutar basa zuba hannun jari da ya kamata a cikin harkar dan inganta aikinsu.

Me magana da yawun Ministan, Bolaji Tunji ne ya bayyana haka inda yace wannan halin rashin ko in kula da kamfanonin Discos din na taimakawa wajan rashin raba wutar yanda ya kamata a Najeriya

Karanta Wannan  Nifa ba da son raina na dawo Najeriya ba, garkuwa dani aka yi>>Inji Nnamdi Kanu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *