
Gamayyar kansiloli sun tsige shugaban karamar hukumar Shira da mataimakinsa ne a dalilin rashin iya jagoranci da rashin sanin makamar aiki, inda kansilolin suke zargin shuwagabannin biyu suna tafiyarda harkokinsu tareda tauye hakkin kansilolin da al’ummarsu
Lamarin ya faru ne a safiyar yau litinin a karamar hukumar mulkin Shira dake jihar Bauchi, inda zuwa yanzu kansilolin sun tura takardar hukuncin a gaban majalisar jihar
Daga Real Buroshi Mawaka Sokoto