Sunday, March 30
Shadow

Karamin yaro dan shekaru 4 ya kkàshè kansa ta hanyar hàrbìn kansa da Bìndìgàr iyayensa da yake wasa da ita a cikin mota

Karamin yaro me shekaru 4 ya harbi kansa da Bindigar iyayensa da ya dauka a mota.

Rahoton yace yaron ya harbi kansa a kai ne.

Lamarin ya farune a Davenport dake jihar Floridan kasar Amurka.

Iyayen yaron Robert Morris da matarsa, Quinta Morris suna shiri ne dan kai ‘ya’yansu zuwa cin Pizza inda shi yaron doki ya kaishi ga har ya rika kowa shiga mota ya zauna yana jiran iyayensa su je.

Matar tana kan Kwamfuta a yayin da Mijin yake bandaki yana wanka a yayin da lamarin ya faru, matar tace ta ji karar abu inda ta yi tsammanin yaranta ne ke kwaramniya.

Ta leka dan ta musu magana amma sai ta tarar da danta me shekaru 11 da me shekaru 7 ne kawai suke wasa.

Karanta Wannan  Donald Trump ya lashe zaben shugaban kasar Amurka

Tan sai ta hango kofar shiga garejin motarsu a bude aikuwa tana lekawa sai ta ga dan nata a kwance, da harbin bindiga akai.

Iyayen sun garzaya dashi zuwa Asibiti, lamarin ya farune ranar Juma’ar data gabata inda yaron kuma ya mutu ranar Asabar.

Jami’in dansanda na Davenport, Chief Steve Parker ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace suna mika ta’aziyyarsu ga iyalan yaron sannan yayi kira ga iyaye dasu kiyaye inda suke ajiye bindigunsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *