
A kwanannan an yi ta gasar komawa jam’iyyar APC tsakanin ‘yan majalisa da gwamnoni.
Saidai akwai manyan masu laifi da ake zargin sun saci kudin Talakawa kuma har hukumar yaki da rashawa da cin hanci EFCC ta fara bincikensu.
Amma tun da suka Koma APC ba’a kara jin labarin binciken da ake musu ba.
Gasu kamar haka:
Godswill Akpabio:
Ana zarginsa da satar kudin jiharsa ta Akwa-Ibom yayin da yayi gwamna da suka kai Naira Biliyan N108.1. Kuma EFCC ta fara bincikensa.
Amma duk da haka ba’a hukuntashi ba, tunda ya koma APC shiru kake ji.
ORJI UZOR KALU
Shima Kalu an kamashi inda aka zargeshi da cin kudin jihar Abia lokacin yana gwamnan jihar.
Har an yanke masa hukunci amma kuma tun da ya koma APC shima shiru kake ji.
STELLA ODUAH
An zargeta da satar Naira Biliyan 5, kuma ana kan shari’arta amma tun da ta koma APC shiru kake ji.
Sauran sune MUSILIU OBANIKORO, da PETER NWAOBOSHI da EMMANUEL BWACHA.
An dai Tuntubi EFCC dan ta yi magana kan lamarin amma sun ki cewa uffan.