
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima yayi kira ga iyalan marigayi, Alhaji Aminu Alhassan Dantata da cewa kada su bari dukiya ta raba kawunansu.
Ya bayyana hakane a yayin ziyarar da ya kai Kanon gidan marigayin a madadin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Kashim yace iyalan su kasance a hade sannan kada su yi fariya kuma su kasance da taimako irin na mahaifinsu.
Yace rashin dantata ba ga iyalansa bane kawai, rashine da aka yi ga dukkan kasa.
Yace me dukiyar kansa ya rasu hakan kawai ya isa wa’azi a gane cewa, babu abinda zai dawwama a Duniya.