Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya bayyana cewa, wutar lantarkin Najeriya zata ci gaba da lalacewa saboda injinan dake samar da wutar duk sun tsufa.
Ministan ya kara da cewa, da kyar suke iya kula da injinan wutar da suka gada daga gwamnatocin baya saboda sun lalace.
Ya bayyana hakane yayin da yake bayani kan yanda ma’aikatarsa zata kashe kudadenta a shekarar 2025 a gaban majalisar tarayya ranar Litinin.
Ministan ya bayyana cewa sau 8 ne kacal wutar Lantarkin Najeriya ta dauke a shekarar 2024 maimakon sau 12 da ake ta yadawa.
Ministan ya kuma kara da cewa, karfin wutar lantarkin Najeriya ya karu da kaso 34 a shekarar 2024.