
Wani da yayi ikirarin shi abokin karatun ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ne ya karyata Ministan kan ikirarin da yayi cewa a mota kirar Mercedes Benz ya rika zuwa jami’a har ya kammala karatunsa.
Mutumin me suna, Allen Wogu ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa, ga su abokan karatun Wike da ransu amma yana son ya rika karya.
Yace su dai basu san Wike ya rika zuwa makaranta da motar Mercedes Benz ba watakila a zuciyarsa ne yake tunanin hakan.
Wike yayi karatu ne a jami’ar Fatakwal watau University of Port Harcourt