Kasar Canada ta sanar da cewa ta aikawa kasar Amurka tallafin jiragen sama masu kashe Gobara a birnin Los Angeles.
Koda a baya, kasar Mexico ma ta kaiwa kasar ta Amurka tallafin masu aikin kashe gobara.
Jimullar masu kashe gobara dubu 14 ne ke aikin kashe gobarar.
Rahotanni sun bayyana cewa, hadda masu laifi dake tsare a gidan yari sai da aka dauko dan su taimaka a kashe gobarar.