
Kasar Iran ta mayar da martani kan sharadin da kasar Amurka ta sanya mata na tattaunawar sulhu da suke kan shirinta na mallakar makamin kare dangi.
Rahotanni sun bayyana cewa, Amurka ta ce Iran zata iya ci gaba da inganta makamashin kare dangi amma a hankali ba da gaggawa kamar yanda take yi a yanzu ba.
Saidai Iran tace ita kasa ce me cin gashin kanta dan haka bata amince da sharadin da Amurka ta gindaya mata ba.
A baya dai hukumar kula da makamashin Nokiliya ta Duniya ta bayyana cewa, Iran ta inganta makamashin Uraniyum zuwa matakin kaso 60 cikin 100 wanda gaf take da ta kai matakin kaso 90 cikin 100 wanda shine zai bata damar mallakar makamashin kare dangi.