
Kasar Pakistan ta bayyana cewa, tana goyon bayan kasar Iran a ci gaba da gumurzun da suke da kasar Israyla.
Pakistan ta yi Allah wadai da hare-haren da kasar ta Israyla ta kaiwa Iran inda a wasu rahotannin ta bayyana cewa, a shirye take ta goyi bayan Iran a wannan rikici.
A jiyane dai yaki ya barke tsakanin Israyla da Iran inda Israyla ta fara kaiwa Iran hari inda ta kashe manyan sojojinta da dayawa daga cikin masana kimiyyar ta.
Kasar dai ta zargi Iran da yunkurin mallakar makamin Kare dangi wanda tace ba zata amince da hakan ba.
Israyla ta kaiwa Iran hare-hare akan tashar inganta makamin kare danginta.
Saidai daga baya itama iran ta yi ramuwar gayya.