
Rahotanni sun bayyana cewa, kasar Rasha na shiryawa kasashen Duniya da basu kai ga gasar cin kofin Duniya ba wasanni na musamman dan cin kofin data sakawa auna Kofin Duniya.
Za’a buga gasar cin kofinne a daidai lokacin da ake buga gasar cin kofin Duniya a shekara me zuwa.
Rasha zata aikata hakanne dan matsawa hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA lamba ta dage mata takunkumin hana shiga gasar cin kofin Duniyar data kakaba mata.
Kasashen da ake tsammanin zasu shiga wannan gasa sun hada da.
Russia, Serbia, Greece, Chile, Peru, Venezuela, Nigeria, Cameroon, China, da sauransu.