
Kasar Saint Lucia ta girmama shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da lambar girmamawa mafi girma a kasar.
Hakan ya farune yayin da shugaba Tinubu ke ziyarar aiki a kasar kuma an karramashi ne dan kokarinsa wajan kyautata zumunta tsakanin kasashen biyu.
Ba kasafai kasar Saint Lucia ke baiwa kowa wannan kyautar karramawar ba wanda hakan ke nuna muhimmancin da shugaba Tinubu ke dashi a wajansu.