
Ministocin harkokin wajen ƙasashen Larabawa sun bayyana rashin jin daɗinsu ga gwamnatin Isra’ila, game da rashin amincewa da tawagar ƙungiyar ƙasashen ta ziyarci yankin da aka mamaye a Gaɓar Yamma da kogin Jordan don tattaunawa da shugaban Falasɗinawa.
A wani taron manema labarai, ministan harkokin wajen Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan Al Sa’ud, ya ce matakin da Isra’ila ta ɗauka kamar watsi ne da tayin zaman lafiya.
A ranar Asabar wani jami’in Isra’ila ya ce batun samar da ƙasar Falasɗinu ne manufar ziyarar.
Cikin wata sanarwar haɗin-gwiwa, ƙasashen Masar da Qatar sun ce za su ruɓanya ƙoƙarinsu don a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
Shugaban ƙungiyar ƙasashen Larabawa da ministoci huɗu sun gana da shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas ta kafar Intanet.