
Gwamnatin tarayya ta koka da cewa, Kaso 85 na daliban Najeriya da take daukar nauyinsu dan zuwa kasashen waje su karo ilimi da zummar su dawo dan ciyar da Najeriya gaba, basa dawowa.
Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a wajan wani taro da ya wakana a Legas.
Yace dalilin haka yasa suka canja lissafi domin sun gano cewa yawanci karatun da ake daukar nauyin daliban su je su yi a kasashen da suka ci gaba, za’a iya yinsa a Najeriya.
Yace dan hakane suka mayar da hankali wajan karfafa harkar ilimin a Najeriya inda yace sun bude cibiyoyin bincike da zurfafa ilimi a jami’o’i daban-daban na kasarnan.