
Matan yankin Niger Delta dana jihohin Inyamurai sun hadu sun gudanar da zanga-zanga inda suke Allah wadai da tonon sililin da Sanata Natasha Akpoti kewa kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio.
Matan sun bayyana cewa, su a yankinsu suna girmama mazansu dan haka ba zasu bari sanata Natasha Akpoti ta wulakanta dansu ba.
Daya daga cikin matan me suna Mrs Grace Mathias da suka fito yin zanga-zangar a garin Uyo na jihar Akwa-Ibom ta gargadi sanata Natasha Akpoti cewa, ko dai ta janye wannan zargi da takewa Sanata Godswill Akpabio ko kuma su duka gwiwowi kasa su roki Allah ya sakko da bulalarsa ya zaneta.
Matar tace wannan shine karo na karshe da zasu bari Natasha ta kara zargin dansu.
Tace ba zau kyaleta ta cimma burinta na wulakanta dansu ba.