Saturday, December 13
Shadow

Kifewar kwale-kwale ta kàshe mutum biyar a jihar Sokoto

Mutum bakwai ne suka rasu sakamakon kifewar kwalekwale a yankin ƙaramar hukumar Shagari da ke jihar Sokoto a arewacin Najeriya.

Lamarin ya faru ne a lokacin da matafiyan suka fito daga Gidan Hussaini zuwa ƙauyen Gwargawu a ranar Litinin da misalin ƙarfe 9:30 na safiya, kamar yadda hukumar bayar da agaji ta ƙasa Nema ta bayyana.

Nema ta ce bayanai sun nuna iska mai ƙarfi ce ta haddasa kifewar jirgin ruwan.

A watan Oktoban 2024 ma wani jirgi ya kife da kusan mutum 300 a yankin Mokwa na jihar Neja da ke tsakiyar Najeriyar. Kafin haka, mutum 24 ne suka mutu a kifewar wani jirgin a watan Satumban 2023 a jihar.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon kala-kala, hadda wadanda baku gani ba na matashiya, Iftihal da aka saba gani da Hijabi amma rana daya sai aka ganta tana rawa da mawaka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *