
Babban me sharhi akan Al’amuran tsaro, Bulama Bukarti ya mayarwa da Tsohon Ministan tsaro, T.Y Danjuma martani kan kiran da yayi mutane su tashi tsaye su kare kansu game da matsalar tsaro.
T.Y Danjuma yace gwamnati ba zata iya ba ita kadai inda yace kamata yayi mutane su tashi su kare kansu.
Saidai a hirar da aka yi dashi a Channels TV, Bulama Bukarti ya bayyana cewa wannan ba mafita bace.
Yace idan aka yi hakan, makamai zasu karu a hannun farar hula wanda hakan zai kawo ci gaba da kisan mutane ba tare da hukunci ba.