
Tawagar tafiyar Atiku Abubakar ta mayar da martani kan maganar komawar wasu ‘yan jam’iyyar PDP zuwa APC ciki hadda mataimakinsa Ifeanyo Okowa a zaben 2023 da kuma Gwamnan jihar Delta Rt. Hon. (Elder) Sheriff Francis Orohwedor Oborevwori.
Tawagar tace sam hakan bai damesu ba kuma be dauke musu hankali ba a kokarin da suke na kwace mulki daga hannun Tinubu ba a shekarar 2027.
Me magana da yawun tafiyar ta Atiku, Salihu Moh. Lukman ne ya bayyana hakan inda yace dama hakan bai zo musu da mamaki dan sun sam dama akwai wadanda kewa Tinubu aiki a cikin jam’iyyar tasu.
Yace nan gaba ma akwai yiyuwar wasu karin Gwamnonin zasu koma APC.
Saidai yace Dimokradiyya kenan, dama ita tana kafuwane a kan gasa.
Yace hakan ba zai dauke musu hankali kan abinda suke na kokarin kafa tafiyar hadaka da zata kawar da Gwamnatin Tinubu ba.