
Hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB ta bayyana cewa, ko da dalibi ya ci jarabawar ta JAMB to ba lallai ya sami damar shiga jami’a ba.
Me magana da yawun hukumar, Fabian Benjamin ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 9 ga watan Fabrairu inda yace samun damar shiga jami’a na bukatar mutum ya samu sakamako na kammala sakandare me kyau da JAMB din da kuma Post UTME.
JAMB ta bayar da wannan amsa ne bayan da iyaye ke ta korafin cewa ‘ya’yansu na rubuta jarabawar JAMB kuma suna ci amma ba’a basu damar shiga jami’a.
Ya kawo misalin wasu iyaye da suka yi korafin an hana ‘ya’yansu shiga jami’a a jihohin Filato da Cross River amma yace daga baya da aka musu bayani sai suka gane cewa ‘ya’yan nasu ne basu cancanci shiga jami’ar ba.
Ya kuma jawo hankalin iyaye dasu fahimci tsarin bayar da admission a jami’o’i dan su daina zargin ana aikata musu ba daidai ba.