
A yayin da tsohon kakakin majalisar dattijai, David Mark ya zama shugaban jam’iyyar hadakar ‘yan Adawa ta ADC, Diyarsa wadda ‘yar majalisar tarayyace, Blessing Onuh ‘yar APC ce.
Hakanan shima dan Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, Watau Bello El-Rufai wanda shima dan majalisar wakilai ne na tarayya, dan APC ne.
Lamarin dai ya jawo cece-kuce inda ake cewa ga iyaye a wata jam’iyya, ‘ya’ya ma a wata jam’iyyar.