
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya baiwa ‘yan Arewa baki inda yace su yi hakuri da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad su koma goyi bayanshi ya sake zama shugaban kasa a shekarar 2027.
Ya bayyana hakane jiya a wajan wani taro da aka yi a Akwanga dake jihar inda yace ko Tinubu mutumin kirkine ko Mugune sai ya kammala mulkin shekara 8 kamin ya sauka.
Yace Arewa ta yi mulki na shekaru 8 dan haka suma kudu sai sun yi mulkin shekaru 8 kamin mulkin ya dawo Arewa.
Yace ‘yan siyasane kawai suke kawo rudani saboda basu samu abinda suke so ba.
Yace a baya wasu gwamnoni sun rika gaya musu cewa Tinubu ne zabin shugaban kasa dan zai gyara Najeriya kamar yanda ya gyara Legas.
Yace amma yanzu sai a canja magana?Yace maganar gaskiya sai Tinubu yayi Takwas.