Friday, May 9
Shadow

Kokarin rage yawan kudaden dake hannun Al’ummar Najeriya da CBN ke yi ya ci Tura maimakon ma kudin dake hannun mutanen su ragu, karuwa suke

Rahotanni sun bayyana cewa matakan da babban bankin Najeriya, CBN ya dauka dan rage yawan kudaden dake hannun ‘yan Najeriya basu bayar da sakamakon da ake so ba.

Babban bankin Najeriya ya dauko matakai masu tsauri sosai dan ganin an rage yawan kudaden dake hannun mutane a Najeriya amma hakan bata samu ba.

Rahoton yace fiye da kaso 90 na tsabar kudin dake yawo a Najeriya na hannun mutanene basa cikin bankuna.

Wanda hakan ke kara nuna cewa mutane sun fi yadda da yin ciniki da kudin zahiri fiye da amfani da banki ko fasahar kasuwanci ta zamani.

Hakan na faruwa ne duk da kokarin gwamnati na karfafa gwiwar mutane wajan rage yawa amfani da tsabar kudi a yayin gudanar da kasuwanci.

Karanta Wannan  Mulkin Tinubu ya talauta masu kudi da yawa>>Inji Atiku

Masana tattalin arziki dai sun bayyana cewa idan kudi suka yi yawa a hannun mutane, kayan masarufi zasu yi tsada, hakanan idan kudi suka yi karanci a hannun mutane, kayan masarufi zasu yi arha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *