
Babbar Kotu a jihar Kano ta yankewa Salisu Idris mazaunin Unguwar Gayawa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta yanke hukuncin a kashe Salisu ta hanyar rataya sakamakon bankawa wata mata da mijinta tare da ɗansu ɗan shekara 2 wuta da yayi sanadiyar mutuwarsu.
Al’amarin ya faru tun a shekarar 25 ga September, 2019 a unguwar Gayawa dake ƙaramar hukumar Ungoggo, a jihar Kano da misalin ƙarfe 2:00 na daren wannan rana.
Mukhtar Abdullahi Shuaibu
Fassara a taƙaice: Bashir Liyafa
Aihanin Rahoton:
DAGA BAKIN MATASHIN DA SUKA KASHE WANI MAGIDANCI DA IYALANSA A KANO
RUNDUNAR Y’AN SANDAN JIHAR KANO TA CHAFKE WANI SAURAYI MAI SUNA SALISU IDRIS DAN SHEKARU 25 DAKE KAUYEN GAYAWA KARAMAR HUKUMAR UNGOGO;
BAYAN SUN ZUBA FETUR SUN KONA WANI MAI SUNA AMINU BALA DAN SHEKARU 50, DA MATARSA DA KUMA Y’AR SU MAI SUNA AISHA.
BAYAN FARUWAR WANNAN LAMARI, KWAMISHINAN Y’AN SANDA YA BADA UMARNI GA DAKARUN Y’AN SANDAN SA CEWA SU TABBATAR SUN CAFKE WADANDA SUKA AIKATA WANNAN TA’ADDANCHI CIKIN AWA 24.
AN KAMO WANNAN MATASHI A GARIN MINJIBIR A INDA YA GUDU WAJEN KAKARSA.
BAYAN AN KAMA WANNAN MATASHI, TARE DA SHAIDAR KUNAN WUTA AJIKINSA, YA SHEDA MANA CEWA, AN YI ALKAWARIN BASHI KUDI DUBU DARI BIYU (N200,000) KAFIN DUBUNSA TA CIKI.