
Rahotanni daga jihar Borno na cewa, Kotu ta daure wasu matasa 2 a gidan yari tsawon shekaru 5 saboda shirya yiwa Gwamnatin jihar Borno zanga-zanga.
Matasan da aka daure sune Mohammed Bukar (Awana)da brahim Mohammed (Babayo).
Rahoton yace mai shari’a Justice A.M Ali ne ya musu wannan hukunci ranar June 30, 2025.
An samesu da laifin shirya yin zanga-zanga da daukar muggan makamai a kafar WhatsApp.