Friday, December 5
Shadow

Kotu ta soke dokar aikin Soja a Najeriya da ta ce dole sai soja yayi shekaru 15 yana aiki kamin a yadda yayi ritaya, Kotun tace soja na da ikon ajiye aiki a duk sanda yake so

Kotun Ma’aikata dake da zama a Abuja National Industrial Court ta soke dokar aikin soja da tace sai soja ya shafe shekaru 15 yana aiki kamin a yadda yayi ritaya.

Kotun tace wannan doka ta sabawa kundin tsarin mulki dannan ta take hakkin sojojin wanda kundin tsarin mulki ya basu sannan ta bayyana dokar da cewa kamar bautar da sojojin ake.

Dan haka tace ta soke wannan doka kuma a ko wane lokaci sojan Najeriya zai iya yin ritaya ya ajiya aiki.

Mai shari’a, Justice Emmanuel D. Subilim ne ya yi wannan hukunci bayan da sojan sama, Flight Lieutenant J. A. Akerele.ya shigar da kara saboda yana son ya ajiye aiki amma an hanashi.

Karanta Wannan  Bidiyo: Tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya samu tarba me kyau a Karamar hukumar Chukun inda ya kai tallar ADC

Sojan yace an ki yi mai karin girma sannan ana ta wahalar dashi a gidan sojan inda wanda suka fara aiki tare an musu karin girma amma shi ba’a mai ba.

Yace dalili kenan ya ajiye aiki amma hukumar sojan tace bata yadda ba sai ya kai shekaru 15 yana aikin kamin a yadda ya ajiye aiki, dalili kenan da ya kai hukumar sojin kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *