
Shugaban sojojin Najeriya, COAS, Lt.-Gen. Olufemi Oluyede ya baiwa sojojin Umarnin su bi duk inda masu yiwa Najeriya barazanar tsaro suke su gama dasu.
Ya bayar da wannan umarnin ne a yayin bikin sallah tare da sojojin a Giwa dake jihar Kaduna.
Maj.-Gen. Erema Akerejola, ne ya wakilci shugaban sojojin a wajan bikin sallar.
Yace biyayya da karfin hali da sojojin Najeriya ke nunawa ya taimaka matuka wajan nasarorin sa suke samu a fagen daga.
Ya kuma jinjinawa sojojin da suka rasa rayukansu a fagen daga inda yace yana baiwa iyalansu tabbacin jajircewar da suka nuna ba zata tafi a banza ba.