Monday, March 17
Shadow

Ku daina baiwa Azzaluman shuwagabannin mu bashi>>NLC ta roki Bankin Duniya da IMF

Kungiyar kwadago ta roki bankin Duniya da kungiyar bada lamuni ta Duniya, IMF da su daina baiwa mugayen shuwagabanni bashi.

Kungiyar tace baiwa irin wadannan shuwagabannin bashi bashi da amfani dan kuwa tana kara rikita harkar mulki ne da kara jefa gwamnatocin wadannan kasashe cikin bashi da rashin ci gaba.

Shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero ne ya bayyanawa hukumomin kudin na Duniya haka inda ya kuma gaya musu cewa shawarwari da suke baiwa Najeriya game da tattalin arzikinta na kara jefa kasar ne cikin talauci da rashin ci gaba.

Joe Ajaero ya baiwa IMF da Bankin Duniyar shawarar cewa su daina bayar da shawarar tattalin arziki ga kasashe a dunkule, su rika bada shawarar da zata rika kawowa kowace kasa ci gaba.

Karanta Wannan  Soyayyar Da Nake Yi Wa Tinubu Da Shettima Ta Sa An Je Har Wurin Sana'ata An Sace Min Turaren Da Nake Siyarwa, Don Haka Daga Yau Na Bar Tafiyar Tinubu/Shettima, Inji Bashir Musa Maiturare Daga Garin Nguru, Jihar Yobe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *