
Shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ‘yan Adawa su gama duk wata hadaka da zasu yi, Tabbas Tinubu ne zai sake zama shugaban kasa a shekarar 2027.
Ya bayyana hakane ta bakin me magana da yawu sa, Oliver Okpala.
Ganduje yace hadakar SDP, Labour Party da PDP babu inda zata je dan kuwa kowane daga cikinsu yana da ra’ayi dabanne dan haka ba zasu samu matsaya ba.
Ya bayyana ‘yan Adawar a matsayin masu son kansu maimakon kishin al’umma.