
Babban Attajirin Najeriya wanda ya mallaki matatar man fetur mafi girma a Nahiyar Africa, Aliko Dangote yacewa ‘yan Najeriya suna cikin Alheri da sa’a dan kuwa suna sayen man fetur a farashi kasa da wanda sauran kasashen Africa ke saye.
Dangote yace farashin man fetur a Najeriya yana ana sayar dashi ne kaso 55 cikin 100 kasa da farashin da ake sayarwa a sauran kasashe.
Watau ‘yan Najeriya na siyan man fetur din a farashib kaso 45 cikin 100 idan aka kwatanta da sauran kasashen Africa.
Dangote yace kuma matatar mansa ta taimaka wajan rage farashin man fetur din a Najeriya daya tsaya a farashin tsakanin Naira 815 zuwa Naira 820 akan kowace lita.
Dangote ya bayyana hakanne a yayin da shugaban Kungiyar ECOWAS, Dr Omar Touray da tawagarsa suka kai mai ziyara matatar tasa.
Yace za’a samu ci gaba sosai idan kasashen Africa suka karfafa kasuwanci a tsakaninsu.