
Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume ya jawo hankalin ‘yan Siyasar Arewa inda yace mada su ce zasu nemi tsayawa takarar shugaban kasa sai nan da 2031 bayan Shugaba Tinubu ya kammala mulki.
Ya bayyana hakane a Arewa House dake Kaduna inda aka yi taron tattaunawa tsakanin shuwagabanni da talakawa.
Yace Tinubu ya dauko alherin aikin da babu inda taba ba.
Yace cire tallafin man fetur ya sa gwamnati ta samu karin kudin shiga sosai inda ake baiwa Gwamnoni suka aikatawa.