Wednesday, January 15
Shadow

Kuma Dai: An kara kara farashin Man Fetur

Rahotanni sun bayyana cewa a yayin da ‘yan kasuwar man fetur ke shirin fara dauko mai daga matatar man fetur ta Dangote gidajen man fetur da yawa sun kara farashin litar man.

Hakan na zuwane bayan da gwamnatin tarayya ta amince ‘yan kasuwar su dauki man fetur kai tsaye daga matatar man fetur ta Dangote ba tare da dillancin kamfanin man fetur na kasa NNPCL ba.

Wasu gidajen man fetur din sun mayar da farashin litarsu zuwa Naira 1,250 inda wasu kuma suka mayar da farashin zuwa 1,300.

Wasu na sayarwa akan farashin 1,150 inda wasu ke sayarwa akan farashin 1230.

Karanta Wannan  Ko kunsan cewa kotu tace a ci gaba da tsare yaran da gwamnati ke zargi da cin amanar kasa sai ranar 1 ga watan Janairun 2025 sannan za'a ci gaba da shari'ar su?

Majiyar Hutudole ta yi hira da wasu masu ababen hawa da suke shan man fetur inda suka rika bayyana rashin jin dadinsu akan lamarin hauhawar farashin man fetur din a kusan duk kwanaki kalilan.

Cire tallafin man fetur dai na nufin kowane dan kasuwa na da damar sayar da man fetur din a farashin da yake so inda hakan zai baiwa mutane damar zabar gidan man da ya fi sauki dan su sayi man.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *