Thursday, December 25
Shadow

Kuma Dai: Bayan X, Hukumar DSS ta kuma aikawa Facebook bukatar kulle shafin Sowore

Hukumar ‘yansandan farin kaya, DSS ta aikawa da kamfanin Meta me mallakar Facebook da bukatar kulle shafin mawallafin jaridar Sahara Reporters kuma me ikirarin kare hakkin bil’adama, Omoyele Sowore.

DSS kamar yanda suka aikawa X sun bukaci cewa, Facebook su kulle shafin Sowore saboda sakon da ya wallafa me cewa shugaban kasa me laifine sannan kuma ya yi karya a Brazil inda yace ya magance matsalar rashawa da cin hanci amma a zahiri bai magance din ba.

DSS kamar yanda suka gayawa X sun ce wannan sakon ya kawo matsalar tsaro da cin zarafi ga shugaban kasa da sauransu.

Saidai Sowore duk da wannan bai nuna alamar nadama ba.

Karanta Wannan  Benjamin Hundeyin ya zama kakakin rundunar ƴansandan Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *