
Rahotannin da hutudole ke samu na cewa bayan Yahaya Zango wanda aka kama jiya a Abuja wanda rikakken dan Bindiga ne da jami’an tsaro suka dade suna nema tare da Alhazai masu shirin zuwa Makkah Aikin Hajji, An sake kama wasu mutane 4 suma a Abujan.
Mutanen da aka kama sun hada da wata mata da ake zargin Mahaifiyace ga dan Bindiga Gwaska Dankarami, da kuma Madele wanda shi kuma mahaifin dan Bindiga Ado Aliero ne sai kuma wani me suna Bello Bazamfare.
Rahoton yace wani kuma da aka kama tare dasu ana zargin dan uwan Ado Aliero.
A shekarar data gabata ma dai an samu rahotannin ‘yan Bindiga 14 da suka je aikin Hajji.