Friday, December 5
Shadow

Kungiyar Dattawan Arewa ta bukaci shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta baci kan tsaro a Arewa

Ƙungiyar dattawan Arewacin Najeriya (NEF) ta buƙaci shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a yankin sakamakon matsalar tsaro da ke ci gaba da ta’azzara wanda ya lalata rayuka da tattalin arzikin ƙasar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar, Farfesa Abubakar Jiddere ya fitar, ƙungiyar ta bayyana damuwarta kan hare-hare da garkuwa da mutane da kashe su ba ƙaƙautawa da ake ci gaba da yi a yankin.

Ya yi gargaɗin cewa idan ba a magance matsalar ba, alummomi ka iya ɗaukar matakin kare kai wanda zai iya kai wa ga ƙazancewar rikicin da kuma kawo cikas ga dimokraɗiyyar ƙasar da zaman lafiyar yankin.

Karanta Wannan  Shahararren Ɗan Kokowar Zamani (Wrestling) Dake Kasar Amurka, Hulk Hogan Ya Mutu Yana Da Shekara 71 A Duniya, Yau Alhamis

“Muna kuma yi kira ga gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakai da dama ciki har da ayyana dokar ta-ɓaci domin ƙara duba girman lamarin, kuma ta aika jam’ian tsaro masu ƙwarewa tare da kayan aiki domin su kare fararen hula da tsare iyakoki.” in ji ƙungiyar.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci “Gwamnati ta bayar da diyya da agaji ga waɗanda lammuran matsalar tsaro suka shafa ciki har da waɗanda suka rasa matsugunansu.”

Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnati ta ɗauki matakan da suka haɗa da ƙarfafa tsaron iyakoki, da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe makwafta cikin ƙungiyar ECOWAS da Tarayyar Afirka domin magance ayyukan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da ke ta’adi kan iyakoki, da kuma haɗa kai da ƙungiyoyin ƙasashen waje kamar Majalisar ɗinkin duniya domin samun tallafi.

Karanta Wannan  ABIN A YABA: Gwamna Abba Kabir Ya Gana Da Iyayen Wasu Yara Almajirai Biyu Da Ya Ci Karo Da Suna Kwance A Bakin Titi Cikin Dare, Inda A Take Cikin Daren Ya Sa Aka Kwashe Su Aka Kai Su Fadar Gwamnati Aka Ba Su Masauki Da Abinci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *