Friday, December 5
Shadow

Kungiyar Kwadago ta kasa, NLC ta baiwa membobinta umarnin su shirya shiga yajin aiki dan goyawa Kungiyar PENGASSAN baya a fadan da take da Dangote

Kungiyar Kwadago ta kasa, NLC ta yi kira ga Membobinta dasu shirya shiga yajin aiki dan giyawa kungiyar PENGASSAN baya game da fadan da take da matatar man fetur din Dangote.

Hakan na zuwane bayan yajin aikin da kungiyar PENGASSAN ta fara wanda ya dakatar da ayyuka a matatar man fetur din Dangote.

Kotun Masana’antu ta dakatar da kungiyar PENGASSAN shiga yajin aikin a ranar lit, saidai PENGASSAN tace bata samu hakan a hukumance ba daga kotun.

A hirarsa da Punchng, shugaban NLC, Joe Ajaero ya bayyana cewa membobinsu su shirya dan fara yajin aikin nuna goyon baya ba kungiyar PENGASSAN inda ya zargi Matatar man fetur din Dangote da samar da tsare-tsaren masu take hakkokin ma’aikata.

Karanta Wannan  Kwamishina a jihar Kano ya ajiye muƙamin sa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *