
Kungiyar Likitocin NARD tace ta baiwa Gwamnatin tarayya awanni 24 ta biya mata bukatunta.
Hakan na zuwane bayan da kungiyar ta baiwa gwamnatin kwanaki 10 wanda suka kare a ranar 10 ga watan Satumba.
Kungiyar ta bayyana hakane bayan zaman taron da ta yi na tsawon awanni 6 ranar Laraba.
Shugaban kungiyar, Dr. Tope Osundara ya tabbatar da hakan inda yace suna sane da alkawarin biya musu bukatunsu da gwamnati ta yi amma suna son gani a kasa.
Kungiyar tace idan a karshen ranar Alhamis basu ga hakkokinsu da suke bi ba, ranar Juma’a zasu tashi da yajin aiki.