Kungiyar Likitocin Najeriya, NMA ta dakatar da aiki a Asibitin Murtala Muhammad dake Kano inda tace likitocin ta su daina aiki a asibitin.
Kungiyar Likitocin ta dauki wannan mataki ne bayan cin zarafin da ta zargi kwamishiniyar jin kai ta jihar, Amina Abdullahi Ganduje da yiwa wata likita.
Kungiyar tace tana neman gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya kori kwamishiniyar daga aiki kamin su koma bakin aiki.
A sanarwar da ta fitar ta bakin shugabanta, Abdurrahman Ali kungiyar tace abin takaici ne lamarin da ya faru ranar 1 ga watan Nuwamba.
Likitar na bakin aiki a bangaren kula da yara inda take kula da yara kusan 100 ita kadai, sai ga kwamishiyar ta shiga wajan inda ta rika cin zarafin likitar akan rashin wani magani da aka rubuta.
Sanarwar kungiyar likitocin tace wannan kuma ba laifin likitar bane dan haka babu dalilin da zai sa a ci zarafinta.