Friday, December 5
Shadow

Kungiyar Manyan ma’aikatan Man fetur, PENGASSAN ta baiwa membobinta umarnin dakatar da aikawa matatar Man Fetur ta Dangote Danyen Mai da Gas, Dangoten ya koka

Rahotanni sun ce kungiyar manyan ma’aikatan man fetur, PENGASSAN sun baiwa membobinsu umarnin su dakatar da aikawa matatar man fetur ta Dangote Danyen Man fetur da Gas.

Kungiyar tace ta yi hakanne da gudanar da addu’a da neman Shuwagabannin Najeriya su takawa Dangote birki kan karan tsaye da yake a harkar man fetur a Najeriya.

Hakan na zuwane bayan da Matatar Dangote din ta sallami ma’aikatan ta 800 bayan da suka shiga lingo PENGASSAN.

PENGASSAN tace Dangote ya dauko indiyawa amma ya kori ‘yan Najeriya 800 da suke masa aiki.

Tace a yayin da ake biyan injiniyoyi ‘yan Najeriya Albashin 385,000 a wata, Indiyawa da Dangote ya dauko yana biyansu albashin dala $5000 ne watau kwatankwacin Naira Miliyan 7.5.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda matar shugaban kasar Faransa ta fallamai mari a bainar jama'a

Kungiyar PENGASSAN ta bukaci Dangote ya mayar da ma’aikatan ‘yan Najeriya da ya kora bakin aikinsu sannan ya dakatar da rashin adalcin albashin da yake musu.

Kungiyar tace babu wani mutum daya da ya fi karfin Najeriya.

Saidai Dangote a bangarensa ya zargi kungiyar ta PENGASSAN da yiwa tattalin arziki Najeriya zagon kasa.

Sannan yace sun son su kawo wahalar man fetur.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *