
Kungiyar Tuntuba ta Arewa, ACF ta bukaci a yiwa Tshàgyèràn Dhàjì irin afuwar da akawa tsageran Neja Delta.
Shugaban kungiyar, Bashir Dalhatu ya bayyana haka a wata hira da kafar Arise TV suka yi dashi.
Ya bayyana cewa, afuwar da akawa ‘yan Neja Delta tasa an dauki nauyin su sun yi karatu sun zo sun zama masu amfanar da al’umma.
Yace hakanan wata matsala da ake fuskanta da irin wadanan mutane itace yanda suke rayuwa babu kayan more rayuwa irin wadanda ake dasu a birane.