Saturday, December 13
Shadow

Kungiyar Yan Kwallon kafa Mata na Najeriya sun koka da cewa, har yanzu ba’a kai ga basu dala $100,000 da shugaba Tinubu ya ce ya basu ba

Kyaftin ɗin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, Rasheedat Ajibade, ta ce har yanzu ba a ba su dala 100,000 da Gwamnatin Tarayya ta yi musu alƙawari bayan sun lashe gasar WAFCON a ƙasar Maroko ba.

Ajibade, ta bayyana takaicinta game da jinkirin biyan kuɗin da aka musu alƙawari.

“Ba mu karɓi kuɗin ba tukunna, amma ina fata za a biya mu. Duk alƙawuran da aka mana, yanzu dai ba mu samu komai ba.”

Ajibade ta jagoranci tawagar zuwa ga nasara, inda suka sake lashe kofin WAFCON a bana.

Bayan nasarar, Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ’yan wasan da masu horar da su lambar yabo ta ƙasa (Officer of the Order of Niger – OON).

Karanta Wannan  Kalli yanda wannan mutumin yawa kansa dan ya daina shan taba

Haka kuma ya yi musu alƙawarin bai wa kowannensu dalar Amurka 100,000 da gida mai ɗaki uku.

Lokacin da ya karɓe su a Fadar Shugaban Ƙasa, Tinubu ya yaba da jajircewarsu, da kuma ƙoƙarinsu, inda ya ce nasararsu ta ɗaga mutuncin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *