
Jigo a tafiyar gamayyar ‘yan Adawa, Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, zasu yiwa sabuwar jam’iyya rijista saboda akwai yiyuwar APC zata hanasu zaman lafiya a ADC.
El-Rufai yace ADC jininsu a kumba yake saboda APC na shirin zuga tsaffin ‘yan jam’iyyar ADC din su musu bore su ce basu yadda da shigarsu jam’iyyar ba.
Yace dan haka ne zasu wa sabuwar jam’iyyar tasu rijista idan ta baci a ADC sai su koma can.
El-Rufai ya bayyana hakane a yayin ganawa da kafar RFI.