
Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa, akwai yiyuwar Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta koma neman bashi a wajan Opay.
Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu na shan suka saboda yawan cin bashi.
Kwanannan ADC ta soki shugaban kasar da cewa, bashin da ake bin Najeriya zai iya kaiwa Naira Tiriliyan 200 nan da watan Disamba.
Sakataren yada labarai na ADC, Mallam Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa bashin da shugaba Tinubu ya ciyo yafi wanda shugaba Buhari yaci.
A hirar da aka yi dashi a Arise TV, Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa, Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta jefa dubban ‘yan Najeriya cikin yunwa duk da yawan bashin da take ciyowa.
Malaye yace be san dalilin da yasa shugaban ke ciwo bashin makudan kudade ba sannan bai san me yasa ‘yan majalisa ke amince masa da ciwo bashin ba.
Yace kuma Gwamnatin ta Tinubu ce wadda tafi barnatar da dukiyar talakawa.
Yace ta yaya za’a ce ana samun kudin shiga masu yawa amma kuma ana ci gaba da ciyo bashi? Melaye yace ba abin mamaki bane nan gaba Tinubu ya fara cin bashi daga Opay da Moniepoint.