Friday, December 26
Shadow

Kwankwaso ya karbi ‘yan APC 1,230 da suka koma jam’iyyar NNPP

Tsaffin magoya bayan Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, sun koma jam’iyyar NNPP daga APC.

Sumaila wanda aka zaba a jam’iyyar NNPC ya watsar da jam’iyyar inda ya koma APC shi da mutanen mazabarsa a watannin da suka gabata.

Saidai magoya bayan nasa a yanzu sun barshi inda suka koma jam’iyyar APC bisa jagorancin Jamilu Zamba inda suka ce ya ci amanarsu.

Masu komawa NNPP din sun fito daga kananan hukumomin Albasu da Sumaila . Akwai kuma wadanda suka fito daga Bunkure da Tofa da sauransu.

Da yake karbarsu a gidansa dake Titin Miler Kano, Kwankwaso ya bayyana cewa ana musu maraba kuma za’a musu adalci a jam’iyyar NNPP.

Karanta Wannan  Kalli Sabon Bidiyon da Sadiya Haruna ta Wallafa inda tace Zawarci ba Dadi ita shaida ce, Sannan ta fashe da dariya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *