Thursday, May 29
Shadow

Labari Me Dadi: Bankin Duniya ya bayar da Dala Miliyan $215 a rabawa Talakawa kyauta saboda halin matsin da ake ciki

Najeriya ta samu karin bashin dala Miliyan $215 daga bankin Duniya wanda ta nema dan rabawa talakawa tallafi kyauta.

Gaba dayan bashin da Gwamnatin Najeriya ta nema dala Miliyan $800 ne wanda tace zata yi amfani dashi wajan rabawa Talakawa kudin kyauta, musamman tsofaffi da masu nakasa da saran masu rauni cikin al’umma.

Tun a shekarar 2021 ne Gwamnatin ta nemi bashin saidai saidai bankin Duniyar be bayar da kudin gaba daya ba.

Yana bayar dasu da kadan kadanne, zuwa yanzu Bankin ya bayar da Jimullar dala Miliyan $530 kenan.

Wannan tallafi dai za’a bayar dashi ne saboda ragewa mutane radadin cire tallafin man fetur dana dala da sauran tsare-tsaren gwamnati da suka jefa mutane cikin halin kaka nika yi.

Karanta Wannan  Dattawan arewa sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara bakin aiki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *