Friday, January 23
Shadow

Labari Me Dadi: Gwamnatin Tinubu zata gina Titin Jirgin kasa irin na kasashen Turai da zai rika yawo a cikin gari a Kano dan rage cinkoso

{“remix_data”:[],”remix_entry_point”:”challenges”,”source_tags”:[],”origin”:”unknown”,”total_draw_time”:0,”total_draw_actions”:0,”layers_used”:0,”brushes_used”:0,”photos_added”:0,”total_editor_actions”:{},”tools_used”:{},”is_sticker”:false,”edited_since_last_sticker_save”:false,”containsFTESticker”:false}

Gwamnatin Tarayya na shirin samar da titin jirgin ƙasa wanda zai riƙa zirga-zirga a cikin birnin Kano don rage cunkoson ababen hawa.

Hon. Abubakar Kabir Abubakar, Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Kasafin Kuɗi ne ya bayyana haka inda ya ce aikin zai ci kimanin Naira tiriliyan ɗaya da rabi.

An shirya wannan aikin ne domin rage cunkoson ababen hawa da kuma samar da wadata ga tattalin arziƙi jihar da zarar an kammala shi.

Hon. Bichi ya kuma bayyana cewa akwai wasu ayyuka da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara a Arewacin Najeriya, waɗanda suka haɗa da gyaran ababen more rayuwa, kiwon lafiya, noma, ilimi, da tsaro.

Karanta Wannan  Najeriya ta zo ta shida a cikin kasashen da aka fi aikata ayyukan tà'àdàncì a Duniya na shekarar 2025

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *