
Najeriya ta yo odar jirgin yaki me suna M-346 guda 24 daga kasar Italiya.
A watan Nuwamba na shekarar 2023 ne hukumar sojin sama NAF ta nemi sayen jiragen daga kamfanin kerasu me suna Messrs Leonardo dake kasar Italia.
Kudin sayen jiragen sun kai €1.2 billion kuma an bayyanasu da cewa shine babban kudi da aka taba kashewa wajan sayen makamai a yankin Afrika ta yamma.
Kamfanin ya amince zai ci gaba da baiwa Najeriya aikin kulawa da jirgin na tsawon shekaru 25.
Jirage 6 na farko tuni aka fara kerasu inda ake tsammanin guda 3 za’a kawo su a 2025 inda sauran za’a kawo su a shekarar 2026.